1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An saki Tandja Mamadou

May 10, 2011

An mayar da martani irin daban-daban dangane da sakin tsofon shugaban ƙasar Nijer Tandja Mamadou da aka yi

https://p.dw.com/p/11DGr
Tsofon shugaban jamhuriyar Nijer Tandja MamadouHoto: picture alliance / dpa

Rahotanni daga birnin Yamai fadar mulkin jamhuriyar Nijer sun nuna cewar kotun ɗaukaka ƙara ta saki tsofon shugaban ƙasar Tandja Mamadou bayan da ya share sama da watanni goma a tsare tun bayan kifar da gwamnatin sa da sojoji suka yi a ranar sha takwas ga watan fabarairu na shekara ta 2010 a sakamakon rikicin siyasar da ya biyo bayan shirinsa na ta zarce. Ga dai ƙarin rahotanni daga wakilanmu a birnin Yamai Gazali Abdu Tasaoua da Mamman Kanta. Sai kuma hira da Yahouza Sadissou Madobi yayi tare da Dr. El-Back Adam, malami a jami'ar Yamai akan sakin na Tandja Mamadou.

Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal

Edita: Zainab Mohammed Abubakar