1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Maduro ya yi wa fursunan siyasa afuwa

Gazali Abdou Tasawa
June 2, 2018

Shugaban kasar Venezuwela Nicolas Maduro ya yi afuwa a jiya Juma'a ga wasu fursunoni 40 akasarinsu 'yan adawa a daidai lokacin da yake fuskantar matsin lamba daga kasashen duniya.

https://p.dw.com/p/2ypiX
Venezuela Vereidigung Präsident Maduro
Hoto: picture-alliance/dpa/Prensa Miraflores/M. Garcia

Shugaban kasar Venezuwela Nicolas Maduro ya yi afuwa a jiyia Juma'a ga wasu fursunoni 40 akasarinsu 'yan adawa kana ya sanar da shirin sakin karin wasu fursunan nan gaba kadan. Shugaban ya bayyana cewa ya dauki wanann mataki ne a wani yinkuri na neman maido da zaman lafiya a kasar bayan takaddamar da ta biyo bayan zabensa. 

Sai dai daura da wannan sakon zaman lafiya, Shugaba Maduro ya yi kashedi ga wadanda ya kira masu kokarin shirya masa makarkashiya. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban ke fuskantar matsin lamba daga kasashen duniya bayan da ya sake lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar a cikin wani yanayi mai cike da cece-kuce.