An saki dukkan ´yan adawa da ´yan sanda suka kame a Zimbabwe | Labarai | DW | 28.05.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An saki dukkan ´yan adawa da ´yan sanda suka kame a Zimbabwe

´Yan sanda a Zimbabwe sun sako dukkan magoya bayan ´yan adawa da aka kame a wami samame da aka kai kan hedkwatar jam´iyar su a karshen makon jiya. Kakakin jam´iyar adawa ta Movement for Democratic Change MDC, Nelson Chamisa ya fadawa kamfanin dillancin labarun AFP cewa an saki sauran mutane 41 daga cikin 200 da aka kame a karshen mako ba tare da an tuhume su ba bayan sun shafe kwanaki biyu a gidan wakafi. A ranar asabar da ta gabata ´yan sanda dauke da manyan makamai suka kutsa cikin hedkwatar jam´iyar MDC a lokacin da ´ya´yanta ke wani taro, inda suka yi awon gaba da mutane 200 galibi matasa. Yanzu haka dai ´yan sandan Zimbabwe sun haramta yin wani gangami na siyasa a babban birnin kasar wato Harare.