1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

An Saki Benezir Bhutto daga daurin talala

Bayan yini guda tana tsare ,da yammacin yau an saki Bhutto

default

Benazir Bhutto

Gwamnatin Pakistan ta sanar da sakin Benezir Bhutto daga daurin talala da ake mata a gidanta.

Mataimakin ministan kula da harkokin yada labaru na Pakistan Tariq Azeem ya bayyana cewar Ɗaurin talala da akayi Bhutto ba wani abu bane face kareta daga harin kunar ɓakin wake ,da wasu yan ta’adda ke shirin aiwatarwa a lokacin da zata jagoranci zanga zangar adawa a kusa das garin Rawalpindi,kuma zaa ɗage wannan tsaron da ake mata ne kowane lokaci daga yanzu.

A yau nedaia jami’an tsaro a kasar ta Pakistan suka tsare harabar gidan tshohuwar prime minista kuma jagorar ‘yan adawa Bhutto,inda suka hanata fita domin jagorantar gangamin adawa da dokar ta ɓacin da shugaba Musharraf ya kafa a wannan kasa tun ranar asabar data gabata.

A hirar da wata kafar yada labarai mai zaman kanta a pakistan tayi da ita,da wayar tanagaraho daga gidanta na Islamabad Benezir Bhutto tace...

“Gwamnati ta bayyana cewar tana kare ni daga ‘yan kunar bakin wake da ake zargi da kasancewa cikin biranen kasar.Tambayata ana itace,Idan har tasan dacewar akwai ‘yan kunar baƙin wake acikin birnin Islamabad,meya hanata kame su?idan har tana sane da cewar akwai wa’yannan yan ƙunar bakin wake a biranen kasar ,to meya hanata cafkesu?”

A hirar datayi tun da farko da wasu magoya bayan jami’iyyarta a bainar ‘yan jarida ,Bhutto ta bayyana cewar,tuni suka kammala tsara shirin komasr da pakistan karkashin mulkin democradiyya cikin lumana,sai gashi abun takaici ya karkace daga dukkan batutuwa da suka tsara tare.

Adangane da kalaman Musharraf na gudanar da zaɓe a ranar 15 ga watan febarairun shekara ta 2008 kuwa,tsohuwar prime ministan tace waɗannan tamkar kalamai ne na yaudara.

A Ɓangarensa ministan kula da harkokin yaɗa labaru Mohammed Durrani,bayyana kalaman yanke dangantaka da shugaba Musharraf da Bhuto tayi,tayi shi ne cikin ɓacin rai.Adangane da hakane yace gwamnati zata cigaba da tattaunawa da ‘yan adawan kasar da suka haɗar da jammi’iyyar PPP ta Benazir Bhutto,duk kuwa da halin da ake ci.

Adangane da wannan hali da ake ciki kuwa kasashen duniya musamman masu alaka da kasar kamar jamus da Amurka sun bayyana cewar zasu sake nazarin dangantakarsu da gwamnatin na musarraf.

Ministan kula da harkokin waje na tarayyar jamus Frank Walter Steinmeier yace jamus zata sake waiwayen makamai da take shigarwa zuwa pakistan din,kana zata tsananta taimako ta fannin ayyukan tattali da takewa alummomin wannan kasa.

Kakakin kakakin hukumar kula da harkokin ketaren jamus Martin Jäger,yayi kira dangane da bukatar sakin Benezir Bhutto..

Yace ayau anyiwa shugabar Adawa a pakistan Benezir Bhuto ɗaurin talala ,ayayinda ake cigaba da cafke yan jami’iyyar adawa,adangane da hakane gwamnatin tarayyara jamus take kira da a saki wadannan mutane,kana a dakatar da daurin talala da akewa Benazir Bhutto.