An saki Aung San Suu Kyi | Labarai | DW | 13.11.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An saki Aung San Suu Kyi

Mahukuntan Birma sun saki Aung San Suu Kyi bayan da suka shafe shekaru suna tsare da ita.

default

Aung San Suu Kyi yayin da take jawabi ga magoya bayanta bayan sakinta.

Mahukunta a ƙasar Burma sun saki Aung San Suu Kyi, 'yar fafutukar aiwatar da dimukuraɗiya a wannan ƙasa. An ga wasu motocin gwamnati da aka tura zuwa gidanta da ke bakin wani ƙogi inda 'yan sanda suka fid da shingayen da aka kewayen gidan da su. Bayan sakinta,  Suu Kyi ta yi jawabi ga dubban magoya bayanta da suka yi dafifi a wajen gidan nata. A cikin shekaru 21 da suka gabata Suu Kyi, wadda ta taɓa samun kyautar zaman lafiya ta Nobel ta shafe shekaru 15 ana tsare da ita. Shugabanni ƙasashen Turai da dama da Amirka da Ƙungiyar Haɗin-kan Yankin Kudu maso Gabashin Asiya su yi madallah da haka.  Acimma sakin Suu kyi ne mako guda bayan da gwamnatin sojan Burma ta lashe zaɓe da gagarumin rinjaye.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas

Edita. Abdullahi Tanko Bala