An saki Abdurrahaman dan kasar Afghanistan mai ridda | Siyasa | DW | 28.03.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

An saki Abdurrahaman dan kasar Afghanistan mai ridda

A sakamakon tabin hankalin da yake fama da shi kotu ta saki Abdurrahaman dake fuskantar shari'ar ridda

An ji bayanin sakinsa ne daga bakin lauya mai daukaka kara da sunan gwamnatin Afghanistan Muhammed Eshaq Aloko a fadar mulki ta Kabul, inda yake cewar:

“An mayar da kundin shari’ar zuwa ga hannun mai daukaka kara da sunan gwamnati sakamakon wasu matsaloli da kuma rashin lafiyar da yake fama da ita. A saboda haka ya zama wajibi mu ba da izini da a sake shi.”

A takaice bayanin na Muhammed Eshaq Aloko na mai yin nuni ne da cewar Abdrrahaman na da tabin hankali kuma a saboda haka aka dakatar da shari’ar da ake masa wanda hukuncinta ya tanadi kisa ga masu laifuka na ridda. Amma a hakikanin gaskiya sakin Abdurrahaman da aka yi yana da nasaba ne da matsin lamba a siyasance da gwamnatin Afghanistan ta sha fama da ita daga kasashen ketare dangane da wannan shari’a ta ridda. Kasashe kamarsu Jamus da Amurka da Kungiyar Tarayyar Turai sun bayyana adawarsu da shari’ar sannan suka kuma yi bara barazanar dakatar da taimakon kudin da take ba wa kasar. Shi ma Paparoma Benedikt na goma sha shida sai da ya sa baki a wannan matsala. A dai halin da ake ciki yanzun ba wanda ya san inda Abdurrahaman yake. Ministan shari’a Sarwar Danish ya ba da sanarwar sakinsa, ko da yake wasu rahotannin sun ce har yau yana tsare a hannun mahukunta saboda tsaron lafiyarsa. Domin kuwa a karshen makon da ya wuce an canza masa gidan kaso sakamakon barazanar kisan kai da ya fuskanta daga sauran fursinoni a inda aka tsare shi da farko. A kuma jiya litinin daruruwan masu zanga-zanga a garin Mazari-i-shariff suka nemi da a yanke masa hukuncin kisa. Da wuya Abdurrahaman ya ci gaba da zama a kasar ta Afghanistan bayan sakinsa da aka yi. An saurara daga kakakin MDD Andrew Edwards yana mai fadin cewar:

“A dai halin yanzu muna tattaunawa mai zurfi da gwamnatin Afghanistan domin neman bakin zaren warware matsalar. Abdurrahaman ya nemi da a ba shi wata mafaka a wajen kasar Afghanistan kuma mun sikankance cewar za a samu wata kasar da zata amince da ta karbi bakoncinsa domin shawo kan matsalar a cikin ruwan sanyi.”

Abdurrahaman dai ya taba zama a nan jamus tsawon shekaru da dama kafin ya tsayar da shawarar komawa gida domin taimakawa wajen sake gina kasarsa.