1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An sake yin mummumar bata kashi a yankin Kashmir

September 1, 2011

Sojoji da dama sun halaka sakamakon musayar wuta tsakanin Indiya da Pakistan a yankin kan iyakar Kashmir.

https://p.dw.com/p/12Rlp
Rigingimu sun zama ruwan dare a Kashimir duk da dakarun tsaro masu sintiriHoto: AP

Rahotannin sun yi nuni da cewa sojoji da yawa ne aka kashe a musayar wuta da ta auku a yankin kan iyakar ƙasashen Indiya da Pakistan. Kowace daga cikin ƙasashen guda biyu na zargin ɗayar da laifin aukuwar wannan faɗa a yankin na Kashmir dake cikin tsaunukan Himalaya. Rundunar sojin Pakistan ta ce an kashe mata dakaru guda uku, sannan jami'an sojin Indiya sun ce sun yi asarar soji ɗaya. Wani kakakin rundunar sojin Indiya ya ce arangamar ta auku ne lokacin da sojojin sa kai na 'yan aware suka yi ƙoƙarin kutsawa cikin yankin Kashmir dake ƙarƙashin gudanawar Indiya. Dukkan ƙasashen biyu na iƙirarin mallakar yankin gaba ki ɗaya amma suna iko ne kaɗai da wasu sassa na sa. A shekarar 2003 suka amince da tsagaita wuta amma an yi ta keta ƙa'idojin shirin. A cikin watan Fabrairu Pakistan da Indiya suka sanar da komawa ga tattauna batun zaman lafiya kan yankin na Kashmir.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Usman Shehu Usman