An sake yin harbe-harbe a wata makaranta a Amirka | Labarai | DW | 03.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An sake yin harbe-harbe a wata makaranta a Amirka

Wani dan bindiga dake harbi irin na kan mai uwa da wabi a jihar Pennsylvania ta Amirka ya kashe akalla wasu yaran mata su 3 bayan yayi garkuwa da wasu ´yan makarantar Kirsta da ake kira Amish. Wasu yara 7 sun samu rauni. Rahoton da ya iso mana yanzu yana cewa yarinya ta 4 ta cika a asibiti sakamakon raunin da ta ji. Da farko dan bindigan yayi garkuwa ne da ´yan makarantar, amma daga bisani ya saki yara maza, kafin ya daure ´yan mata ya fara harbinsu daya bayan daya. Wannan lamarin na daga cikin munanan harbe harben da aka fuskanta a makarantun Amirka cikin mako guda kacal.