An sake yin awon gaba da maaikatan mai a Najeriya | Labarai | DW | 04.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An sake yin awon gaba da maaikatan mai a Najeriya

Akalla maaikatan 5 ne yan bindiga sukayi awon gaba da su a yankin Naija Delta dake taraiyar Nijeriya.

Jamian maaikatar mai sunce an sace wadannan mutanen 4 ne daga Eket,kuda da kanfanin mai na Mobil.

A halin da ake ciki dai mahunkuntan Nijeriya sunce suna iyakar kokarinsu domin an ganin an sako wasu yan kwangila 16 na kanfanin shell da suka bace bayan harin da kungiyoyin yankin suka kai ranar litinin.

Tuni dai an sako maaikatn kanfanin shell su 9.

Wata gamaiyar kungiyoyn yan gani kashe na yankin ta dauki alhakin kai wannan hari ta kuma bukaci a sako shugabanta Mujahid Dokubo Asari dake jiran sharia akan zargin da ake masa na yiwa kasa zagon kasa.