An sake sallamar wani hafsan sojin ƙasar Jamus | Labarai | DW | 13.03.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An sake sallamar wani hafsan sojin ƙasar Jamus

Ministan tsaron Jamus ya sallami ƙarin wani hafsan sojin ƙasar bisa abin da ya shafi harin watan satumban bara a Afganistan

default

Ministan tsaron Jamus da ruddunar sojin ƙasar

Ta bayyana cewa ministan tsaron ƙasar Jamus Karl-Theodor zu Guttenberg ya sake sallamar wani hafsan sojin ƙasar, a wani abinda ya shafi harin da sojojin ƙasar Jamus suka bayar da umarnin kaiwa a yankin Kunduz na ƙasar Afganistan, kuma ya hallaka jama'a da yawa. Ma'aikatar tsaron ƙasar ta tabbatar ta da cewa an sallami Birgediya Janar Henning Hars daga aiki. Janar Hars wanda tsohon jami'in tarone a offishin jakadancin Jamus dake a birnin Washington na Amirka ya rubutawa ministan tsaron Jamus wasiƙa, inda ya yi suka bisa sallamar man'yan hafsoshin soji na ƙasar da aka yi. Janar ɗin ya kuma buƙaci ministan da ya sake duba batun harin na watan satumban bara wanda ya hallaka 'yan Afganistan142 akasari fararen hula. Mawallafi: Usman Sheh Usman