An sake kashe mutum daya a musayar wuta tsakanin Fatah da Hamas | Labarai | DW | 19.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An sake kashe mutum daya a musayar wuta tsakanin Fatah da Hamas

An sako dukkan ´ya´yan kungiyar Fatah da na Hamas wadanda wasu ´yan bindiga dadi suka yi garkuwa da su a karkashin wani shiri a tsakani. A jiya daddare aka mika kusoshin membobin Fatah su 8 da takwarorinsu na Hamas guda 4 ga masu shiga tsakani don yin sulhu. Duk da shirin tsagaita wuta tsakanin kungiyoyin biyu, an kashe mutum daya a wata musayar wuta da sassan biyu suka yi a birnin Gaza. A kuma halin da ake ciki FM Falasdinawa Isma´il Haniya ya ce zai gabatar da wani muhimmin jawabi a yau talata don mayar da martani ga kira da shugaba Mahmud Abbas yayi na shirya sabbin zabuka na gaba da wa´adi. An samu hauhawar tsamari tsakanin bangarorin biyu bayan da Abbas ya ba da sanarwar cewa zai kira sabbin zabuka da zumar kawo karshen gwagwarmayar rike madafun iko da ake samu karkashin gwamnatin da Hamas ke wa jagora.