An sake kashe dakarun Amirka guda 7 a Iraqi. | Labarai | DW | 16.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An sake kashe dakarun Amirka guda 7 a Iraqi.

Hukumar rundunar sojin Amirka a Iraqi ta ba da sanarwar yin asarar sojojinta guda 7 a fafatawar da suka yi da ’yan yaƙin gwagwarmayar ƙasar a yankuna daban-daban.

Sanarwar, wadda aka buga yau a birnin Bagadaza, ta ce an kashe sosjoji biyu daga rundunar mayaƙan ruwan ƙasar ne jiya a wani ɗauki ba da daɗin da ba ta bayyana inda ya auku ba. Sojojin na daga wani rukunin rundunar ne da ke girke a garin Falluja a yammacin Iraqin. Har ila yau dai, wani soja ɗaya kuma ya sheƙa lahira ne, yayin da wani bam da aka tayar a gefen titi ya ragargaza motar da yake ciki a arewacin Bagadaza. A jihar Kirkuk, inda nan ma ’yan yaƙin gwagwarmayar Iraqin suka kara da rukunan sojojin ƙetare, sanarwar ta ce dakarun Amirka biyu ne suka mutu, sa’annan wasu biyu kuma suka ji rauni, a wannan fafatawar. Sa’annan wasu sojoji biyu da suka ji munanan raunuka a wani ba ta kashin da aka yi a jihar Salaheddin, su ma sun mutu a asibiti, inji sanarwar. Gaba ɗaya dai, a cikin wannan watan kawai, sojojin Amirka 57 ke nan aka kashe a ɗauki ba daɗi tsakaninsu da ’yan yakin gwagwarmaya a Iraqin.

Tun da Amirka ta afka wa ƙasar a cikin watan Maris na shekara ta 2003 kawo yanzu kuma, yawan sojojinta da aka kashe a Iraqin ya kai dubu biyu da ɗari 7 da 66, inji wasu alƙaluman da kamfanin dillancin labaran nan AFP ya bayar yau, waɗanda ke matashiya da ƙididdigar da ma’aikatar tsaron Amirkan, wato Pentagon ta buga.