1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan sanda sun sake kama Besigye na Yuganda

Yusuf BalaFebruary 19, 2016

Sakamakon da ya fira fita na nuni da cewa shugaba Moseveni na da kashi 63 cikin dari na kuri'un da aka kada na zaben shugaban kasar ta Yuganda.

https://p.dw.com/p/1HyYO
Uganda Rukungiri Kizza Besigye beim Wahllokal
Besigye a kan gaba magoya baya na biye da shiHoto: Getty Images/AFP/STRINGER

'Yan sanda a kasar Yuganda sun sake garkame madugun adawa a kasar Kizza Besigye sannan sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa gangami na magoya bayansa bayan da aka fara bayyana sakamakon zaben da ke nuna cewa shugaba Yoweri Museveni ya tasamma ci gaba da rike madafun iko bayan shekaru 30 a kan kujerar mulki.Sakamakon da ya fira fita na nuni da cewar shugaba Moseveni na da kashi 63 cikin dari na kuri'un da aka kada, sakamakon da tuni Basigye da wasu 'yan adawar ke ganin an tafka magudi a cikinsa. Shi dai shugaba Moseveni ana zarginsa da kama karya da ma sanya kasar cikin yanayi na samun koma baya a fannin tattalin arziki ga rashin aiki musamman a tsakanin matasa.

'Yan sanda a birnin na Kampala dai sun harba hayaki mai sa hawaye a shelkwatar jam'iyyar FDC da Basigye ke mata takara, bayan kuwa a jiya ana ganin an kada kuri'un zabe lafiya.