An sake kai wani mummunan harin bam a Bagadaza | Labarai | DW | 01.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An sake kai wani mummunan harin bam a Bagadaza

Akalla mutane mutane 66 sun rigamu gidan gaskiya sannan kimanin 70 sun jikata a wani harin bam da aka kai da mota a unguwar Sadr City ta ´yan shi´a dake birnin Bagadaza. ´Yan sanda da kuma ma´aikatar cikin gida sun ce bam din ya fashe ne a lokacin da wata motar sintiri ta ´yan sanda ta kutsa cikin wata kasuwa dake cike da jama´a. Daukacin wadanda suka rasu ko suka jikata dai fararen hula ne. Wannan harin dai shi ne mafi muni a Iraqi a cikin watanni 3. A kuma halin da ake ciki tashar telebijin ta Al-jazeera mai watsa shirye shiryenta da harshen Larabci ta rawaito cewar wata kungiyar fafatuka a Bagadaza ta yi garkuwa da wata ´yar majalisa ´yar sunni da masu tsaron lafiyarta su 8.