1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An sake kai harin bam a ƙasar Aljeriya

Akalla mutane 28 sun rasu sannan wasu dama sun samu raunuka sakamakon tashin wani bam da aka dana cikin mota a kusa da wani barikin jami´an gadin gabar tekun kasar Aljeriya. Kamfanin dillancin labarun kasar ya rawaito jami´ai na cewa an kai harin ne a garin Dellys da ke arewacin kasar. Garin dai na da tazara kilomita 50 daga Aljiyas babban birnin kasar. Wannan harin ya zo kwanaki biyu bayan wani harin kunar bakin wake da aka kai kan wani gungun mutane dake jirar isar shugaba Abdelaziz Bouteflika a wata ziyarar da ya kai a garin Batna. Akalla mutane 20 suka rasa rayukansu a wannan hari.