An sake kai harin ƙunar baƙin wake a birnin Kabul | Labarai | DW | 02.10.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An sake kai harin ƙunar baƙin wake a birnin Kabul

Majiyoyin ´yan sanda a Afghanistan sun ce akalla ´yan sanda 12 aka kashe sannan wasu 15 sun samu raunuka a wani harin kunar bakin wake da aka kai a Kabul babban birnin kasar. Dan kunar bakin wake ya ta da bam a cikin wata bas dake dauke da jami´an ´yan sanda dake kan hanyar zuwa wani wuri dake tsakiyar birnin na Kabul. Wannan harin shi ne irinsa na biyu da aka kai a Kabul a cikin kwanaki 4. A ranar asabar da ta gabata wani dan kunar bakin wake mai shekaru 28 ya halaka sojoji 28 da fararen hula 2. ´Yan tawayen kungiyar Taliban masu tsattsauran ra´ayin Islama sun yi ikirarin kai harin.