An sake kai hari kasar Yemen | Labarai | DW | 16.05.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An sake kai hari kasar Yemen

Wani dan harin kunar bakin wake ya hallaka mutane da dama a wata cibiyar jami'an tsaro da ke kasar Yemen.

Wani dan kunar bakin wake ya tayar da bam a garin Mullaka na kudancin Yemen abin da ya hallaka mutane da dawa yayin da wasu suka samu raunika. Lamarin na wannan Litinin ya faru a helkwatar hukumomin tsaron da ke birnin.

Wannanna zuwa ne kwana daya bayan kusan mutane 50 sun hallaka lokacin hare-hare biyu na tsagerun kungiyar IS masu fafutuka.

Daya daga cikin hare-hare an kan tawogar wani janar na kasar mai suna Mubarak al-Oubthani, wanda ya samu raunika yayin da masu kare lafiyarsa suka hallaka. Kasar ta Yemen tana fuskantan tashe-tashen hankula daga kungiyoyin tsageru masu kai hare-hare.