An sake kai hari kan sansanin sojin Jamus a Kundus | Labarai | DW | 08.10.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An sake kai hari kan sansanin sojin Jamus a Kundus

Kwanaki biyu bayan wani harin kunar bakin wake da aka kai kan wani ayarin rundunar sojin Jamus a Afghanistan, an sake kai wani hari akan sansanin su da ke garin Kundus na arewacin Afghanistan. Wata sanarwa da ma´aikatar tsaron Jamus ta bayar ta ce rokoki 4 suka afkawa sansanin. Ko da yake babu wanda ya jikata a wannan hari da kuma musayar wutar da ta biyo baya amma sansanin ya lalace. A harin kunar bakin waken da aka kan su a ranar juma´a, sojojin Jamus 3 suka samu raunuka. Ministan tsaron Jamus Franz Josef Jung ya bayyana harin da cewa wani yunkuri na dagula al´amura a dangane da kuri´ar da majalisar dokokin Jamus zata kada kan tsawaita aikin sojojin kasar a Afghanistan.