An sake halaka wani bako a Rasha | Labarai | DW | 20.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An sake halaka wani bako a Rasha

Wasu matasa da ba´a gane su sun halaka wani dan asalin China bayan sun daba masa wuka a birnin Mosko. Kamfanin dillancin labarun Interfax ya rawaito ´yan sanda na cewa wadanda suka shaida abin da ya faru sun ce sun ga wasu matasa da suka aske kansu kuma ke sanye da takalma irin na soji, wato irin salon shigar da masu kyamar baki da nuna wariyar launin fata kan yi, sun kai wa dan China din mai suna Li Shi Veng hari. An gano Li mai shekaru 33 da haihuwa a mace sakamakon raunuka na sukar wuka a jikinsa da kuma kan sa. ´Yan sanda da a halin yanzu suka kaddamar da bincike sun ce ba su sani ba ko wannan kisa na daga cikin matsalar hare haren da ake kaiwa baki wanda ya zama ruwan dare a cikin kasar ta Rasha.