An sake halaka fararen hula a hare haren kungiyar NATO a Afghanistan | Labarai | DW | 07.07.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An sake halaka fararen hula a hare haren kungiyar NATO a Afghanistan

Shugabannin kabilu a Afghanistan sun ce fararen hula fiye da 100 aka kashe a wani harin bam da dakarun kungiyar kawance ta NATO suka kai a yammacin kasar. Su kuma mazauna a kauyukan dake cikin tsaunuka na yankin arewa maso gabashin Afghanistan sun ce an halaka ´yan kasar su 25 a wani farmaki ta sama da dakarun kasa da kasa suka kai. To sai dai jami´an ma´aikatar tsaron Afghanistan sun ce watakila wannan hari ya rutsa da wasu fararen hula amma yawan su bai kai yadda mazauna yankin suka nunar ba. a kuma halin da ake ciki dakarun Amirka sun ce sojojin Afghanistan dake samun kariyar dakarun kawance sun kashe ´yan tawayen Taliban 30 a lardin Uruzgan dake kudancin kasar.