1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An sake gwabza kazamin fada tsakanin ´yan tawaye da sojin Chadi

December 9, 2006
https://p.dw.com/p/BuYf
Sabon fada ya barke tsakanin ´yan tawayen Chadi da dakarun gwamnati a kewayen garin Biltine kwana daya bayan da rundunar soji ta sake kwace karamin garin dake gabashin kasar. Wani jami´in gwamnatin Chadi ya fadawa kamfanin dillancin labarun AFP cewar da sanyin safiyar yau fadan ya barke tsakanin dakarun gwamnati da ´yan tawaye. Jami´in ya ce dakarunsa sun kashe ´yan tawaye masu yawan gaske. To amma wani madugun ´yan tawaye ya ce dakarun gwamnatin sun yi ta kansu ne, bayan wani mummunan fada da aka gwabza a yankin a farkon wannan mako. Ya ce an yiwa dakarun gwamnatin kawanya inda suka yi ta kokarin kare kansu.