An sake ganawa tsakanin Olmert da Abbas a Birnin Ƙudus | Labarai | DW | 10.09.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An sake ganawa tsakanin Olmert da Abbas a Birnin Ƙudus

FM Isra´ila Ehud Olmert da shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas sun amince da nada wasu tawagogi biyu wadanda zasu yi kokarin warware muhimman batutuwan da ake takaddama kai gabanin babban taron kasa da kasa kan yankin GTT wanda Amirka zata dauki nauyin gudanarwa. Shugabannin biyu sun cimma wannan yarjejeniya yayin wani taro da suka yi yau a birnin Kudus. Wani jami´in Isra´ila ya ce wakilan tawagogin guda biyu zasu tattauna akan batutuwan da suka shafi tattalin arziki, makamashi da kuma ruwa. To sai dai ba ce komai ba dangane da muhimmin batun na na shata kan iyakokin wata kasar Falasdinu da za´a kafa nan gaba, da makomar ´yan gudun hijirar Falasdinawa da kuma takaddamar da ake akan Birnin Kudus.