1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An sake ganawa tsakanin Olmert da Abbas a Birnin ƙudus

August 28, 2007
https://p.dw.com/p/BuCv

FM Isra´ila Ehud Olmert da shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas sun gana a birnin Kudus inda suka tattauna dangane da batun samar da kasashe biyu makwabtan juna a kokarin samun maslaha dangane da rikicin yankin GTT. Gidan radiyon Isra´ila ya rawaito tawagogin mahalarta taron na cewa shugabannin biyu sun kuma tattauna dangane da shata iyakokin wata kasar Falasdinu da za´a kafa nan gaba, sai kuma batun ´yan gudun hijiran Falasdinu da kuma makomar Birnin Kudus. To sai dai ba´a samu kusantar juna ba. Babban jami´in Falasdinu a shawarwarin da ake yi Saeb Erekat ya ce tattaunawar ta yau ba ta yi tsawo ba.