An sake dage sharar Saddam | Labarai | DW | 24.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An sake dage sharar Saddam

An dage sauraron shariar Saddam Hussein wanda ya kamata a koma a yau talata,zuwa ranar lahadi,kamar dai yadda kakakin kotun,Raed Jouhi ya baiyanawa manema labarai da suke zaune na saoi da dama suna jiran a fara shariar tasa.

Yace wasu daga cikin masu bada shaida suna kasashen ketare,wasu kuma har yanzu basu komo daga aikin hajji da suka tafi ba.

Dage ranar ya zo ne a dai dai lokacinda sabon babban alkali da zai shugabanci shariar zai karbi ragamar shariar daga hannun Rizgar Amin wanda yayi murabus yana mai kokawa da matsin lamban siyasa,inda aka zabi Raouf Abdelrahman.

Lauyoyin da suke kare Saddam da sauran wadanda ake zargi tare da shi su 7,sunce zasu bukaci a dakatar da sauraron shariar saboda janyewara Amin da kuma cewa tsoma baki da gwamnati takeyi ya nuna cewa kotun wanda Amurka ta dauki nauyinsa ba shi da cikkakken yancin kansa.