1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An sake dage sauraron shari´ar da akewa Saddam Hussain

March 1, 2006
https://p.dw.com/p/Bv6I

Tsohon shugaban kasar Iraqi, Saddam Hussain yace shi kadai ya isa ya amsa duk wasu tambayoyi da ake son yi masa a game da yadda mulkin sa ya gudana.

Wannan bayanin dai yazo ne a lokacin da tsohon shugaban ya amsa laifin cewa ya taba bayar da umarnin kai hari ga wasu gonaki na mutanen da aka tabbatar nada hannu a kokarin kashe shi a shekara ta 1982.

Bayanai dai sun nunar da cewa a zaman kotun na yau, masu gabatar da kara sun gabatar da bayanai da kuma hotuna na bidiyo, a kokarin da suke na tabbatar da cewa Saddam Hussain nada hannu a cikin kisan kiyashin da akayiwa shi´awan nan 148, a zamanin mulkin sa.

Zaman kotun na yau ya gudana na a cikin zulumi da dar dar, na hasashen kara barkewar rikici na kabilanci a kasar, wanda a yan kwanakin nan mutane sama da dari suka rasa rayukan su.

An dai dage sauraron shari´ar ta Saddam da Mukararraban nasa bakwai izuwa 12 ga watan nan da muke ciki