An sake ɗage zaɓen shugaban ƙasa a Lebanon | Labarai | DW | 11.01.2008
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An sake ɗage zaɓen shugaban ƙasa a Lebanon

An sake ɗage zaɓen shugaban ƙasa na gobe Asabar har a Lebanon har sai ranar 21 ga watan Janairu. Wannan shine karo na 12 da ake ɗage zaɓen duk kuwa da ƙoƙarin da Ƙungiyar Ƙasashen Larabawa take yi na ganin cewa shugabanin adawar sun amince da shawarar larabawa game da rikicin siyasar ƙasar. Kakakin majalisa Nabih Berri ya sanarda da ɗage zaɓen bayan masu rinjaye da ke da goyon bayan ƙasashen yammacin duniya da kuma yan adawa da ƙungiyar Hezbollah ke jagoranta sun gagara cimma matsaya guda. Tun dai a watan Nuwamba ne kasar ta Lebanon ta kasance babu shugaban ƙasa.