1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An sake ƙulla yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Fatah da Hamas

January 4, 2007
https://p.dw.com/p/BuVa

Jam´iyar Fatah ta shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas da abokiyar gabarta wato Hamas sun sake cimma wata sabuwar yarjejeniyar tsagaita wuta. Yarjejeniyar ta kuma tanadi yin musayar firsinoni tsakanin su. Da farko kuwa an kashe akalla mutune biyar sannan 9 sun jikata a wani kazamin fada da aka fafata a Zirin Gaza. Daga cikin wadanda suka mutu akwai jami´an tsaron Fatah guda 3 wadanda aka harbe har lahira a wata musayar wuta da aka yi a tsakanin ´ya´yan Fatah da na Hamas a garin Khan Yunis. Gabanin musayar wutar jami´an tsaron Falasdinu sun umarci dukkan ´yan kasashen waje da su fice daga Zirin Gaza sakamakon garkuwar da aka yi da wani dan Peru ma´aikacin kamfanin dillancin labaru na AFP.