An sace yan kasar Sudan 6 a Iraqi | Labarai | DW | 23.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An sace yan kasar Sudan 6 a Iraqi

An sace wasu yan kasar sudan 6 a Iraqi,ciki har da wani jamiin diplomasiya.

Wani kakakin maaikatar harkokin wajen kasar yace an sace mutanen 6 ne jim kadan bayan sallar jumaa a yau,cikinsu har da sakataren ofishin jakadancin Sudan Abdel Minam al Dur a birnin Bagadaza.

Mai magana da yawun maaikatar harkokin wajen Jamal Muhammad Ibrahim ya fadawa gidan telebijin na Aljazeera cewa baa sanko suwa suka sace yan kasar ta Sudan ba,amma yayi kira da a sako su ba tare da bata lokaci ba,inda yace su ba yan siyasa bane kuma basu da alaka da wata siyasa da zai bada hurumin sace su.