1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An sace wata 'yar kasar Jamus a Somaliya

Zulaiha Abubakar
May 3, 2018

Wasu mutane dauke da makamai sun sace wata jami'ar lafiya 'yar asalin kasar Jamus a Mogadishu babban birnin kasar Somaliya a yammacin jiya Laraba. Jami'ar dai na aiki ne da hukumar bada agajin ta Red Cross.

https://p.dw.com/p/2x4ku
AFGHANISTAN-UNREST-KIDNAPPING
Hoto: Getty Images/AFP/A. Karimi

Wata sanarwar da aka fidda ta ce hukumar na cikin juyayin abin da ya samu jami'ar wacce ke aiki kullum don ceto wa tare da inganta lafiyar jama'ar da yakin kasar ya jefa a mawuyacin hali, daga nan sai ta bayyana cewar da misalin karfe takwas ne maharan suka kutsa harabar hukumar Red Cross din da ke Mogadishu inda suka sace matar.

Red Cross din ta ce a halin yanzu ta na tattaunawa da hukumomi daban-daban don ganin an sako jami'ar. Kasar Somaliya da ke fama da tada kayar baya ta masu kaifin kishin addini ta kasance sansanin kungiyar ta'addanci ta Al-Qa'ida tun a shekara ta 2005 lamarin da ya mayar da kasar mafi hadari ga jami'an da ke bada agaji 'yan kasashen ketare.