An sace wata mata a yankin Naija Delta | Labarai | DW | 08.02.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An sace wata mata a yankin Naija Delta

Rundunar yan sanda a Najeriya ta sanarda sace wata mata yar kasar Filipins da wasu yan bindiga sukayi jiya a birnin Fatakwal dake yankin Naija Delta.

Wata mai magana da yawun yan sandan tace yan bindigar sunyi awon gaba da matar ne a lokacinda ta fito daga motarta zata shiga wani banki.

Sace wannan mata ya kawo yawan yan kasashen waje da kungoyoyin suka sace zuwa mutum 30 a yankin na naija Delta.

Wannan kuma shine karo na farko tsageran yankin suka sace mace tun lokacinda suka fara garkuwa da yan kasashen waje a yankin.