An sace tsohon Firaministan Libiya
August 14, 2017Talla
Wasu 'yan tawaye a Libiya sun yi awon gaba da wani tsohon Firaministan kasar Ali Zidan. Shi dai Ali Zidan da ke zaune a Tripoli babban birnin kasar, ya shiga hannun 'yan tawayen ne lokacin da yake ganawa da wasu manyan jami'an tsaro. Akwai ma wadanda ke ganin mutanen na da alaka da magoya bayan bangaren gwamnatin kasar da Malisar Dinkin Duniya ya amince da shi.
Babu dai wani karin haske a hukumance kan waje ko halin da tsohon Firaministan na Libiya ke ciki. Cikin watan Oktoban shekara ta 2013 ma dai an taba yin garkuwa da Ali Zidan, kafin daga bisani aka sako shi.