An sace maaikatan mai 4 a Nigeria | Labarai | DW | 14.08.2006
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Labarai

An sace maaikatan mai 4 a Nigeria

Jamian tsaro a tarayyar Nigeria sun tabbatar da sake jamian kanfanonin mai na ketare guda 4 a birnin port hacourt dake yankin Niger Delta,wanda ke kudancin kasar.Rahotanni daga yankin dai na nuni dacewa wadanda aka sacen sun hadar da Ba Amurke guda da dan kasar Britaniya,a wurin shatawarsu a daren jiya.

To sai dai kawo yanzu kakakin rundunar yansanda Irejua Barasua,bata bayyana wadanda keda alhakin sace maaikatan man ba,kuma babu wani kame da akayi adangane da hakan.A daren jiya nedai aka cafke jamian na kasashen ketare,bayan gurnanin bindigogi,daya tilasta mazauna porthacourt din kasancewa a gidajensu.To sai sai a yau din ne kuma aka saki yan kasar Philiphines guda 3 daga cikin wasu jamian mai na ketaren ,10 da ake garkuwa dasu a yankin na Niger Delta mai albarkatun man petur a kudancin tarayyar Nigeria.

 • Kwanan wata 14.08.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammed
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu5z
 • Kwanan wata 14.08.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammed
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu5z