An rusa Super Eagle | Labarai | DW | 30.06.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An rusa Super Eagle

Shugaban Najeria ya sanarda haramtawa ƙungiyar ƙwallon ƙafan ƙasar shiga duk wata gasa a wajen kasar har shekau biyu

default

'Yan wasan Super Eagle

Shugaban ƙasar Najeriya Goodluck Jonthan, ya ɗauki tsauraren matakai kan ƙungiyar ta Super Eagle domin bayyana fushinsa dama na sauran 'yan Najeriya bisa abinda ya faru a Afrika ta kudu, don haka shubana yace ya dakatar da ƙungiyar ƙwallon ƙafar ƙasar daga shiga duk wata gasa a wajen ƙasar har na tsawon shekaru biyu. A wata sanarwa da kakakin shugaban ƙasar ya fitar, ya shaidawa manema labarai cewa. ganin yadda ƙungiyar Super Eagle ta kasa taɓuka wani abu a gasar cin kofin duniya da ke gudana a ƙasar Afirka ta kudu, ya zama tilas a haramta musu shiga du wata wasa, har sai an yi gyaran da yakamata. Ita humar ƙwallon ƙafa ta duniya wato FIFA dama tana zargin sabakin yan siyasa a harkar ƙwallon Najeriya, kuma wannan matakin yana iya tabbatar da hakan. Wakilin Deutsche Welle dake Abuja Uwais Abubakar Idris, ya bayyana cewa ɗaukar matakin da shugaba Jonathan ya yi, ya biyo bayan rohoton da komitin da ya kafa don duba rashin taɓu wani abu da 'yan wasan Najeriyan suka yi a Afirka ta kudu, kasancewa wannan shine karo na farko da aka buga gasar cin kofin ƙwallon ƙafa na duniya a nahiyar Afirka.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Ahmadu Tijjani Lawal