An rufe wasu bankuna a Najeriya | Labarai | DW | 03.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An rufe wasu bankuna a Najeriya

Babban bankin Najeriya,ya rufe wasu bankuna 13 da suka kasa cimma kaidar da bankin ya shimfida musu ta, ko dai su kara yawan jarin bankunansu ko kuma suyi hadaka da wasu bankunan zuwa karshen shekara ta 2005.

A karshen mako ne wasu bankunan na Najeriya su 25 yawancinsu masu zaman kansu, suka cimma wannan kaida ta tara naira biliyan 25 dala 188 ke nan, ko kuma suka hade da wasu bankunan domin cimma wannan adadi.

A dai ranar 6 ga watan yuli na 2004 ne babban bankin Najeriya,ta baiwa bankunan ciniki na kasar su 79 wadannan kaidoji.

Tun farko dai nan bankuna na bukatar naira biliyan 2 ne kacal kafin su fara aiki.

Gwmanan babban bankin Najeriyar Charles Soludo,kwanan nan kuma ya sanrda cewa zaa mika sunayen yan Najeriaya da kuma hukumomi da suke da dimbin basusukan bankunan a kansu, ga hukumar yaki da cin hanci da karbar rashawa da kuma rundunar yan sanda domin a gurfanar da su.