1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An rattaba hannu kan yarjejeniyar yaki da fataucin mutane a Afirka

July 7, 2006
https://p.dw.com/p/BurJ
Ministoci 26 daga kasashen yammaci da tsakiyar Afirka sun sanya hannu kan wata yarjejeniya don karfafa yaki da fataucin ´yan Adam, wanda ke haddasa kwadagon yara da kuma ci da gumin su a wannan yanki da ma a wajen sa. An sanya hannu kan yarjejeniyar ne yau juma´a a gun babban taron hadin guiwa a birnin Abuja tsakanin kungiyar ECOWAS ta yammacin Afirka da kuma takwararta ta ECCAS. Kasashen sun yi alkawarin karfafa ba juna hadin kai a fannonin da suka shafi komawa da wadanda ake fataucin na su zuwa gida tare da kame masu aikata wannan laifi kuma a tasa keyarsu zuwa kasashen su na asali. A cikin wata sanarwar hadin guiwa da suka bayar kungiyoyin biyu sun bayyana yaarjejeniyar da cewa ta tarihi ce domin ta hada dukkan kasashen yammaci da kuma tsakiyar Afirka. Ko da yake babu wani adadi da aka bayar amma babban sakataren kungiyar ECOWAS Mohammad Ibn Chambas ya kiyasce cewar mutane kimani dubu 200 zuwa dubu 800 ake fataucinsu a kowace shekara a wannan yanki.