1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An rattaba hannu kan dokar ceto tattalin arziƙin Turai.

May 22, 2010

Jamus ta amince da shirin ceto darajar kuɗin euro.

https://p.dw.com/p/NV0c
Shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel, tare da ministan kuɗi, Wolfgang Schaeuble, yayin muhawara akan shirin ta da komaɗar kuɗin euro.Hoto: AP

Shugaban Jamus, Horst Koehler ya rattaba hannu kan dokar samar da euro biliyan 750 domin ceto tattalin arziƙin Turai, wadda tuni majalisun dokokin ƙasar guda biyu suka rattaba hannu akanta a jiya juma'a. 'Yan majalisa daga ɓangaren shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel, su ne suka kaɗa ƙuri'ar amincewa da ɗaukar wannan mataki a ƙaramar majalisar dokoki da kuma babbar majalisa ta Bundestag. Sai dai kuma Merkel, ta gaza samun goyon baya daga jam'iyun adawa guda uku waɗanda tun da farko suka yi fatali da wannan doka. A ƙarƙashin wannan yarjejeniya, Jamus za ta keɓe euro biliyan 150 a matsayin tabbaci inda ragowar wannan tallafi za ta fito daga hannun asusun ba da lamuni na duniya da sauran ƙasashen da ke amfani da kuɗin euro.

Mawallafiya: Halima Abbas

Edita: Zainab Muhammad Abubakar