1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An rataye tsohon mataimakin shugaban Iraqi

March 20, 2007
https://p.dw.com/p/BuPD

A safiyar Talatan nan aka aiwatar da rataye tsohon mataimakin shugaban kasar Iraqi a zamanin Saddam Hussaini Taha Yasin Ramadan a birnin Bagadaza. Ɗan sa Ahmad Ramadan yace zaá yi janaizar mahaifin sa a birnin Tikrit kusa da kabarin Saddam Hussaini. A ranar litinin Lauyoyin Taha Ramadan suka baiyana cewa an sanar da su zaá rataye shi a safiyar Talata. Wata kotun Iraqin ta yankewa Taha Yasin Ramadan hukuncin ɗaurin rai da rai bisa samun sa da hannu a kisan yan shiá 148 a garin Dujail a shekarun 1980, to amma daga baya wata kotun ɗaukaka ƙara ta zartar masa da hukuncin kisa ta hanyar rataya.