An rataye tsoffin Jami´an marigayi Saddam Hussain | Labarai | DW | 15.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An rataye tsoffin Jami´an marigayi Saddam Hussain

Rahotanni daga Iraqi sun shaidar da kisan tsoffin jami`an Marigayi Saddam Hussain, wadanda aka yanke musu hukuncin kisa tare.

An dai rataye Barzan Ibrahim Altikrit, dan Uwan marigayi Saddam Hussain da kuma Awad Hameed Al Bandar, ne da kusan wayewar garin yau litinin.

Rahotanni dai sun rawaito cewa Hameed Al Bandar, ya kasance tsohon jami`an leken asiri kuma tsohon shugaban kotun kolin kasar a zamanin mulkin marigayi Saddam Hussain.

Dukannin su guda biyu dai an yanke musu hukuncin kisa ta hanyar rataya ne a watan daya gabata, bayan samun su da laifin hannu a kisan gillar da akayiwa wasu shi´awa 150 a garin Dujail a shekara ta 1982.