1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An rataye fursunoni 42 a Iraki

Abdul-raheem Hassan
September 25, 2017

Ma'akatar shari'ar kasar Iraki ce ta zartar da hukunci rataya kan fursunonin, bayan da aka tuhumesu da laifukan fyade da yin garkuwa da jami'an tsaro hada da dana bama-bamai da ya halaka fararen hula a fadin kasar.

https://p.dw.com/p/2kgoA
Irak Abū Ghuraib Exekutionsraum mit Galgen
Kotun Iraki ta zartar da hukuncin rataya kan wasu fursunoniHoto: Getty Images/S. Platt

Majalisar shura ta kasar Iraki ce ta aiwatar da hukuncin kisan a gidan yarin Nasiriyah da ke kudancin kasar, inda aka baiwa iyalai da sauran dangin mamatan damar zuwa harabar gidan yarin dan ban kwana da yan uwan nasu kafin aiwatar da kisan.

Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Amnesty International, ta yi Allah wadai da hukuncin kisa ta hanyar rataya da hukumomin Iraki suka zartar a kan fursunonin 42. Amnesty ta ce Iraki ta aiwatar da hukuncin kisa mafi girma baya ga kasashen Chana da Iran da kuma Saudiya.