An rantsar da shugaban gwamnatin wucin gadi na kasar Bangladesh
January 12, 2007Talla
An rantsar da tsohon shugaban babban bankin Bangladesh a matsayin sabon shugaban gwamnatin wucin gadin kasar. Fakhruddin Ahmed wanda tsohon ma´aikacin bankin duniya ne, ya yi rantsuwar kama aiki ne a wani buki da aka yi a fadar shugaban kasa dake birnin Dhaka. Shi ya maye gurbin Iajuddin Ahmad wanda a jiya alhamis ya yi murabus. Kafin ya sauka ya shugaba Ahmad ya dage zaben ´yan majalisar dokoki da ake shirin gudanarwa a ranar 22ga watan nan na janeru sakamakon zanga-zangar da kawance ´yan adawa ya shirya. ´Yan adawar na zargin cewa za´a tabka magudin zabe. A kuma halin da ake ciki an girke karin dakarun soji da na ´yan sanda a fadin kasar ta Bangladesh bayan dokar ta baci da aka kafa.