An rantsar da shugabaMwai Kibaki na Kenya | Labarai | DW | 30.12.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An rantsar da shugabaMwai Kibaki na Kenya

A jiya lahadi hukumar zabe ta kasar Kenya ta sanar da sake zaben shugaban kasar mai ci yanzu Mwai Kibaki a matsayin shugaban kasa,bayan zaben da akayi kusan kunnen doki tsakaninsa da shugaban adawa Raila Odinga,wanda ya zargi Kibaki da magudin zabe.