An rantsar da shugaba Idriss Deby na Tchad | Labarai | DW | 08.08.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An rantsar da shugaba Idriss Deby na Tchad

Yau ne a birnin N´Djamena na ƙasar Tchad, a ka yi bikin rantsar da shugaban ƙasa Idriss Deby Itno, bayan zaɓen da ya lashe a watan Mayu da ya gabata.

Shugabanin ƙasashen Afrika da dama, wanda su ka haɗa da na Sudan, Umar El Bashir su ka halarci bikin.

Danganta tsakanin Sudan da Tchad, ta fuskanci ƙarin taɓarɓarewa a lokacin shirye shiryen zaɓen Tchad, inda yan tawaye su ka kai farmaki, a N´Djamena, da burin kiffar da shugaba Idriss Deby.

Hukumomin Tchad, sun zargi Sudan da tallafawa yan tawaye.

A dangane da haka, su ka yanke shawara katse hulɗoɗin diplomatia da Khartum.

Ranar 26 ga watan da ya gabata,, su ka cimma yarjejeniyar sasanta rikicin.

Sanarwa daga fadar mulkin Khartum, ta bayyana cewar, shugaba El Beshir, zai wuce zuwa birnin Dakar na ƙasar Senegal, inda za su shirya taro,sasanta juna, da Shugaba Idriss Deby ,bisa gayyatar Abdullahi Wade, wanda shima a yanzu ke birnin NDjamena.

Saidai, daga ɓangaren hukumominTchad, babu sanarwar da ta bayyana haka.