An rantsar da sabuwar Majalisar dokokin Turquia
August 4, 2007Yau ne a ƙasar Turquia, ake rantsar da sabuwar Majalisar dokoki,wadda jam´iyar Praminista Tayib Recep Erdowan ke da gagaramin rinjaye a cikin ta.
Idan dai ba a manta ba, ranar 22 ga watan da ya gabata hukumar zaɓe, ta bayyana sakamakon zaɓen a hukunce, inda jama´iyar AKP ta sami kujeru 341 daga jimlar kujeru 550 da majalisar ta ƙunsa.
Sannan jam´iyar CHP ta zo sahu na 2, tare da yan majalisa 99.
A karon farko jam´iyar ƙurdawa ta samu kujeru 20,matsayin da ya zama wani abun tarihi a fagen siyasar Turquia.
Masharahanta a game da harakokin siyasar Turquia na tunanin cewar, Kurdawa sunshafui wannan majalisa, bisa dukkan alamu a dalili da matsin lambar da Turquia ke sha daga ƙetare.
Babban yaunin da ya rataya akan yan majalisar a halin yanzu shine, na zaɓen saban shugaban ƙasa.