An rantsar da sabuwar gwamnatin Palestinu | Labarai | DW | 17.03.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An rantsar da sabuwar gwamnatin Palestinu

Majalisar dokokin Paletinu ta kaɗa ƙuri´ar amincewa da sabuwar gwamnatin haɗin kann kasa.

Tun lokacin girka hukumar Palestinawa, a shekara ta 1994 wannan itace gwamnatin farko da ta ƙunshi ministocin ƙungiyoyin Fatah da na Hamas a sakamakon yarjejeniyar da su ka cimma a birnin Makka, a watan da ya gabata.

A jawabin da ya gabatar shugaban hukumar Palestinawa Mahamud Abbas yayi kira ga ɓangarorin 2, da dukan al´ummomin Palestinu su juya baya ga tashen-tashen hankulla, su kuma fuskanci alƙibla guda, ta gina Palestinu, da kuma ƙwato yancin ta , cikin haɗin kai.

Shi kuwa Praminista Ismael Hanniey kira yayi ga ƙasashe masu hannu da shuni su ɗage takunkummin da su ka ƙargamawa Palestinu yau da shekara guda da ta wuce.