1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An rantsar da sabon shugaban kasar Indonesia--

Jamilu SaniOctober 20, 2004

Sabon shugban kasar Indonesia Yudhoyono yayi alkawarin farfado da tattalin arzikin kasa---

https://p.dw.com/p/BvfO
Hoto: AP

A kasar Indonesia yau laraba aka rantsar da Bambang Yudhoyono a matsayin shugban kasar na shida,wanda kuma yayi alkawarin bulo da sabin matakai na farfado da tattalin arzikin kasa tare kuma da yaki da matsaloli na karbar rashawa da kasar ta Indonesia ke fuskanta yayin kuma da sabon shugaban kasar ta Indonesia ya lashi takobin yaki da matsaloli na aiyukan ta’adanci da suka dade sun adabar wanan kasa ta yankin Asia data kowace kasa yawan alumar musulmi a duniya baki daya.

Cikin jawabin da sabon shugaban kasar ta Indonesia yayi ga alumar kasa jim kadan bayan rantsar da shi bisa karagar mulkin Indonesia,Yudhoyono ya bada gargadin cewar gwamnatinsa zata dauki matakan da suka dace na ceto kasar da cikin dumbun matsalolin da take fuskanta.

Tun da farko dai an rantsar da Yudhoyono da mataimakinsa Yusuf Kalla a wani gagarumin biki da aka gudanar bisa tsauraran matakai na tsaro.

Bikin dai na rantsar da sabon shugaban kasar Indonesia da mukadashinsa,ya sami halartar shugbanin kasahen wanan yanki,ciki kuwa har da PM kasar Australia John Howard.

Fiye da jami’an tsaro da suka hadar da yan sanda da soji 2,000 aka tura wurin bikin rantsar da sabon shugaban kasa,da nufin murkushe boren yan kungiyar Jemaah Islamiya ta kasar dake da alaka da kungiyar al-Qaeda da aka zarga da laifin harin bomb din da ya afku cikin watan Octoban shekara ta 2002 a tsibirin Bali,da kuma hari na baya bayan da suka kai ofishin jakadancin kasar Australia dake birnin Jakarta.

A yau din dai kungiyar hadin kann turia ta aika sakonta na taya murna ga sabon zababan shugaban kasar Indonesia Susilo Bambang Yudhoyono ,inda kungiyar ta Eu ta yi alkawarin hada da gwamnatinsa wajen shawo kann matsalolin da suke ciwa kasar ta Indonesia tuwo a kwarya.

Kungiyar ta Eu ta bada sanarwar cewar zata aika wasu daga cikin ministocinta zuwa birnin Jakarta a ranekun 27-28 ga wanan watan da muke ciki zuwa birnin Jakarta,don tabatar da ganin an sami habakar dangantaka tsakanin kungiyar hadin kann turia da kasar Indonesia.

Ita kuwa hukumar yaki da karbar rashawa ta Transprency International cewar ta yi har yanzu kasar Indonesia na zaman daya daga cikin kasahen da matsaloli na karbar rashawa suka yawaita,don haka ne suka yi fatan cewar sabon shugaban kasar Indonesia zai samar da sabin sauye sauye da zasu kawo karshen matsaloli na karbar rashawa da kasar ke fuskanta.