An rantsar da sabin hukumomin Thailand
September 22, 2006Sojojin da su ka gudanar da juyin mulki ranar talata da ta wuce a Thailand, sun samu tabaraki daga sarkin ƙasar.
Bayan ayar dokar da ya sa ma hannu , a yau ɗin nan, aka gudanar da shagulgullan rantsar da sojojin, a matsayin sabin hukumomin da za su jagorancin ƙasar Thailand.
Kamar yadda al´ada ta tanada, saban Praministan, Jannar Sonthi Boonyaratglin, ya sunkuya gaban butun-butumin sarkli domin yi masa mubai´a da da´a.
A nasa ɓangaren hambararen Praminstan,wanda a halin yanzu, ke cikin gudun hijira a kasar Engla, ya rungumi ƙaddara, ya ce kuma a shire ya ke, ya ajje takara, inda aka tashi shirya saban zaɓe.
Saidai Sabin hukumomin ƙasar sun ɗauki mattakai masu tsauri, ga yan siyasa, inda a halin yanzu a ka haramta duk wasu tarruruka na siyasa a fadin ƙasar baki ɗaya.