An rantsar da saban Praminista a Guinee | Labarai | DW | 01.03.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An rantsar da saban Praminista a Guinee

A birnin Conakry na ƙasar Guinee, an yi bukin rantsar da Lansana Kouyate, a matsayin saban Praminista.

Idan daio a na tune ranar litinin da ta wuce, shugaban ƙasa Lansana Konte, ya amince da wannan naɗi, bayan tashe-tashen hankula da su galabaita ƙasar, wanda su ka yi sanadiyar mutuwar mutane kussan 120.

A yayin da ya ke jawabi, saban Praministan ya nunar da babban aikin da ke gaban sa, na tada komaɗar tattalin arzikin ƙasa, da haɗa kann yan ƙasa da kuma shinfiɗa dokokin inganta, tsarin muklin demokradiya.

Lansana Kouyate, yayi kira ga yan Guinee baki ɗaya, su ba shi haɗin kai, don cimma wannan buri.

Saidai an yi wannan shagulgulla, ba tare da halartar shugaban ƙasa ba, Lansana Konte.