An rantsar da mace ta farko shugabar kasa a nahiyar Africa | Labarai | DW | 16.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An rantsar da mace ta farko shugabar kasa a nahiyar Africa

A dazu dazun nan ne aka rantsar da Ellen Johnson Sirlef a matsayin shugabar kasar Liberia , wacce ta kasance mace ta farko data shugabanci wata kasa a nahiyar Africa.

An dai gudanar da rantsuwar ne a karkashin jagorancin babban jojin kasar, wato Me Henry Reed.

Jim kadan da rantsar da ita, Ellen Jonhson Sirlef tayi alkawarin yin aiki kafada da kafada da bangaren adawa na kasar don sake gina kasar ta Liberia.

Daga cikin manyan baki da suka halarci bikin rantuwar sun hadar da mai dakin shugaba Bush , wato Laura Bush da sakatariyar harkokin wajen Amurka CL da kuma shugaba Thabo Mbeki na kasar Africa ta kudu.

Ellen Johnson Sirlef, ta samu wannan narasar ne bayan ta doke abokin karawar ta, wato George Weah a zagayen zabe na biyu da aka gudanar a watan nuwamba na shekarar data gabata.

Ya zuwa yanzu dai da yawa daga cikin masu nazarin siyasa na ganin cewa babban kalubalen dake gaban sabuwar shugabar ba zai wuce neman hadin kann yan kasar ba wajen sake gina ta bayan tasha fama da yake yaken basasa.