1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An rantsar da Bashar Al Assad a wani saban wa´adi na shekaru 7

Majalisar dokokin Syria ta rantsar da shugaban kasa bashar Al-Assad, a wani saban wa´adin mulki na shekaru 7.

A jawabin da ya gabatar gaban yan majalisar, Bashar Al Assad ya bayyana aniyar sa, ta ci gaba da gudanar da ayyukan kyauttata makomar al´lummar Syria da kuma kare yancin ƙasar daga barazanar da ta ke fuskanta daga wasu ƙasashen ƙetare.

A game da rikicin Isra´ila da Syria shugaba Al Assad ya, ya yi kira ga hukumomin Tel Aviv, su bayyana ƙarara aniyar su, ta samar da zaman lahia a mai ɗorewa.

Tun shekara ta 2000 tantanwar tsakanin ƙasashen 2 ta watse baran-baran.

Syria na buƙatar sake mallakar yankunan ta, na tuddan Golan, da Israi´la ta mamaye, tun shekara ta 1967.

A yayin da ya ke huruci a game da saban wa´adin mulkin na Bashar Al Assad, Wadah Abdu Rabo, shugaban jaridar Al watan mai zaman kanta a Syria na mai cewa.