An rantsad da wani tsohon Janar a muƙamin Firamiyan wucin gadi na ƙasar Thailand. | Labarai | DW | 01.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An rantsad da wani tsohon Janar a muƙamin Firamiyan wucin gadi na ƙasar Thailand.

Shugabannin gwamnatin mulkin soji ta ƙasar Thailand, ta naɗa Janar Surayud Chulanont, tamkar firamiyan riƙon ƙwarya na ƙasar. A yau ne dai aka rantsad da firamiyan a wani bikin da aka gudanar a birnin Banngkok. Zai gaji muƙamin tsohon Firamiyan ƙasar Taksin Shinuwatra ne, wanda sojojin suka hamɓarar a wani juyin mulki ta hannunka mai sandan da suka yi a ran 19 ga watan jiya. Hukumar sojin ta ce sabon Firamiya Chulanont zai tafiyad da harkokin gwamnati ne har zuwa lokacin da aka kammala aikin samad da sabon kundin tsarin mulkin ƙasa. Sai dai har ila yau, ba ta bayyana lokacin da ƙasar za ta dawo ƙarƙashin mulkin dimukraɗiyya ba.